Tarihin Manzon Allah (S.A.W)

AdamsDUT

Tarihin Manzon Allah (S.A.W)

Books & Reference
  • 0.00
(0 votes)

Free Install

100000

app installs

Android 4.1+

minimal version

With ads

advertisement

20.07.2017

release date

Recent changes:

Bug fix

Description:

Wannan application yana dauke da tarihi na Annabi Mohammead (S.W.A), wanda wani shahararen marubucin tarihi ya wallafashi da harshen larabci.Shine aka fassara shi izowa harshen hausa domin amfanarwa ga al'umar Hausawa wadan da ke neman ililmi akan cikeken tarihin Manzo Allah (S.W.A).
Littafin ya kunshi gundrin rayuwar Manzon Allah tunda ga kan haihuwar sa, da kuma irin gwagwarmayar da yasha kafin a fara saukar masa da wahayi. Littafin bai tsaya nan ba kadai,ya kara bamu asali da kuma tarihi na mussulunci tunda daga kan annabi na farko, wato annabi Adam (AS) zuwa sauran annabawa a takaice.shi dai wannan littafi yafi bada karfi akan kafuwar musulunci da kuma rayuwar Annabi Mohammad (S.A.W).
ina fatan wannan application wanda akayi shi don sauwakin amfani zai zamo abin amfanarwa ga al'umar musulmi.
Don Allah idan har kajin dadin amfani da wannan application kayi kokari ka yadashi don wasu suma su amfana.

Takaiccen tarihin manzon Allah.

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan ʿAbdullahi (Sallallahu ʿalaihi wa sallam).

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in.

Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi.

Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma waxanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a voye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi xauki ba daxi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.

Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi xan Akhdabl.

'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faxima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMuxallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Xalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.

AdamsDUT other Apps

Download