Wannan na nufin ke nan sai mu fara neman alkaluman da suka dace domin gano yadda girman wadannan hadurra da ke faruwa galibi a daki kuma a kan gado yake.
Bari mu fara da wannan tambaya, kamar yadda yawanci suka yi da saduwa kawai tsakanin namiji da mace ba tare da sanya wani abu na kariya ba ( kororo); ya hadarin yadda wannan saduwa za ta kare da ciki yake?
Wannan bisa dalilan da aka sani ba abu ne mai sauki ba a iya nazarinsa a dakin bincike na kimiyya.
Kamar yadda aka ga wani bincike da aka yi a New Zealand, inda aka bukaci wadanda suka shiga binciken su yi jima'i sau daya kawai a wata, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka fice saboda sun kasa bin wannan ka'ida.
Watakila alkaluman da za mu ce sun dan fi kusanci da ingantattu su ne na wani nazari da aka yi a Turai wanda ya kunshi matasan ma'aurata ( miji da mata) 782.
Dukkanin ma'auratan sun rika tattara bayanan saduwar da suke yi ta kullum ba tare da wani magani ko kariya ta daukar ciki ba, har sai da aka sami juna biyu 487.
Hanya mafi sauki da za a iya kiyasin damar daukar ciki ita ce a yi amfani da wa'adin da aka sadu sau daya kawai (misali a ce a wata daya ko wata biyu da sauransu).
Lokacin da aka fi damar daukar ciki ga alama yana kasancewa ne kwanaki biyu kafin kwan halitta na mace ya je mahaifarta inda zai hadu da na namiji idan an sadu.
A wannan lokaci damar daukar ciki kashi 25 ce cikin dari kamar yadda kididdiga ta tabbatar a baya.
Amma bayan wannan lokacin kuma damar sai ta ragu matuka zuwa kashi biyar cikin dari kawai a sauran kwanakin wannan lokaci.
A takaice jima'i sau daya a tsakanin matasa yawanci zai iya samar da ciki ne a ma'arauta daya a cikin ashirin.
Wannan na nuna cewa damar za ta iya zuwa a kowa ce rana, ba sai wata rana takamaimai ba, domin wadannan abubuwa sun fi faruwa ne a yayin da kake matashi.