Wato Kasar Nijar dai ta kasan ce tana daya daga cikin kasashen Afrika ta yamma.Tana makwabtaka da kasashe bakwai (Nijeriya, Libya, Aljeriya, Mali, Burkina Faso, Benin, Cadi). Tana da al'umma da ta kai fiye da mutum miliyan sha bakwai(17). Kuma tana da kabilu daban-daban, kamar su: Hausawa, Zabarmawa, Fulani, Kanuri, Bugaje, Barebari, Larabawa, Tubawa, da Gurmawa. Nijar ta na daya daga cikin kasashen kungiyar tattalin arzikin kasahen yammacin Africa (CEDEAO).
Nijar ta samu ƴancin kan ta a shekarar 1960 daga Turawan mulkin mallaka na Faransa. Tana da arzikin ma'adani caking kasa kamar Zinariya, da Karfe, da Gawayi, da uranium da kuma Petur
Notice :
This app is develop for education and research purpose and fall under fair use law .