A takaice kalmar Shi’a kalma ce ta larabci, wadda ke nufin ‘mabiya’ ko ‘mataimaka’, wannan kuwa shi ne ma’anarta na lugga. Amma so tari ana amfani da ita a kan duk wanda ya fifita Imam Ali dan Abi Dalib (AS) a kan sauran Sahabbai da wanda ya mika wilayarsa gare shi. Wannan shi ne ma’anar kalmar a muhawara da zantukan yau da kullum. Wannan shi ne abin da malaman lugga suka dace a kai. Firuz Abadi yace:
Shi’ar mutum (na nufin) mabiyansa da masu taimaka misa…..
Har zuwa inda ya ce:
Amma hakika wannan kalma an fi amfani da ita a kan duk wanda ya mika wilayarsa ga Ali (dan Abi Dalib) da mutanensa, har kalmar ta takaita da su.